Bayyana wannan kudurin ya haifar da zazzafar muhawarar tunanin halalta haramtattun abubuwa a Najeriya.
Shugaban hukumar kididdigar Prince Adeyemi Adeniran, ya ce lokaci ya yi da za a fadada tattalin arzikin kasar ya hada da duk lamuran da hada-hadar kudi ke shiga don samar da bayanai da za su zama jagora ga hukumomi wajen tsara hanyoyin gudanar da kasa bisa sahihan alkaluma.
NBS ta ce a wasu kasashe, har mata masu yawon gantali ba aikin saba doka ba ne, don haka kai tsaye ana samun alkaluman kudin da ake amfani da su a wannan bangare amma Najeriya za ta kara bincika sassa irin su tonon ma’adinai ba bisa ka’ida ba don tattara bayanan tsare-tsare da a za su amfani kasa.
“Idan mutane ba su san hakikanin bayanai na tashin farashin kaya a tattalin arziki ba, ba za su san yanda za su yi tsare-tsaren kashe kudin su yanda ya dace ba” Inji shugaban sashen alkaluman farashin kaya na NBS Dokta Ayo Andrew Anthony
Wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya, ya ruwai to cewa, babban jami’i a sashen mizanin arzikin kasa na NBS Ibrahim Yakubu Tanko ya ce "ba gwamnatin Najeriya ne kadai ke amfani da alkaluman da mu ke samarwa ba, hatta bankin duniya, hukumar lamuni ta IMF da ma masu shigowa don zuba hannun jari.”
Har ila yau, Nasiru ya ce, shi ma babban jami’in sashen kula da farashin kayan masarufi CPI na NBS Habib Shehu Usman, ya ce akwai sauyi da za a samu don kayan da a zamanin baya a ke amfani da su sun sauya kamar daina amfani da talabijin marar kala, amfani da wayar salula; amma duk da haka, kayan abinci aka fi bukata a “rukunin kayan da mu ke duba farashin su da ya karu daga 740 zuwa 934.”
A saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya:
Dandalin Mu Tattauna