Bayan kwashe fiye da watanni biyar tana nazarin korafin da aka gabatar gabanta game da rikicin masarautar Kano, kotun daukaka kara ta Najeriya dake Abuja, tace tabbatar da sauke Alhaji Aminu Ado Bayero daga kan karaga da babbar kotun jihar Kano ta yi ya saba tanade tanaden dokoki.
A hannu guda kuma kotun ta ce kotun tarayya da ke Kano ba ta da hurumin sauraron batun daya shafi masarautu
A ranar 15 ga watan Yulin bara ne, babbar kotun Kano karkashin jagorancin mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta tabbatar da matakin gwamnatin Kano na rushe masarautun 5 na jihar Kano da kuma sauke dukkanin sarakunansu
Sai dai sarkin Kano Aminu Ado Bayero da wasu daga cikin sarakunan da aka sauke sun tafi kotun daukaka kara ta Abuja kuma a Juma’ar nan ce kotun ta yanke hukunci akan korafin na su.
A hukuncin su, alkalan kotun bisa jagorancin mai sharia Muhammad Mustafa sun rushe dukkanin abubuwan da babbar kotun Kano ta zartar, tare da cewa kotun ba ta baiwa Sarkin Aminu Ado Bayero dama ya kare kan sa ba gabanin yanke hukunci.
A don haka sai alkalan kotun daukaka karar ta Abuja suka umarci babbar jojin Kano ta mika wannan batu gaban sabon alkali domin ya sake sabuwar shari’a.
Alhaji Musaddiq Wada Waziri, guda cikin makusantan mai martaba Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya ce sun yi maraba da hukuncin kotun daukaka karar ta Abuja.
Sai dai da wakilin mu na Kano Mahmud Ibrahim Kwari ya tuntubi Alhaji Mannir Sanusi na bangaren Sarkin Kano Muhammad Sanusi yace ba a zo gabar da za suyi Magana ba tukunna.
A can baya dai Alhaji Aminu Babba DanAgundi, Sarkin Dawaki Babba shine ya shigar da kara gaban kotun yana kalubalantar cewa, sauke sarki Aminu Ado Bayero ya shafi ‘yancin sa, saboda kujerar sa ta Sarkin Dawaki Babba.
Yanzu haka dai, masana shari’a da dokokin sun fara tsokaci dangane da makomar wannan rikici na masarautar Kano a gaban kotuna, inda Farfesa Nasiru Adamu Aliyu SAN ke cewa, duk da wannan hukunci, Alhaji Aminu Babba DanAgundi na da hurumin daukaka kara zuwa zuwa kotun koli.
Dangane da rusa hukuncin babbar kotun Kano da kotun daukaka karar tayi kuwa, masanin shari’ar yace ci gaba da sauraron shari’ar tare da yanke hukunci da kotun tayi bayan lauyoyin Sarki Aminu sun bayyana janye hannun su daga batun ya sanya tilas kotun daukaka kara ta rusa hukuncin saboda an yi shari’a babu wakilcin sarkin.
Kimanin watanni 10 kenan Sarakuna 2 ke ci gaba da ikirarin mallakar masarautar Kano, yayin da Alhaji Aminu Ado Bayero ke gudanar da harkokin fada a fadar sarki ta Nasarawa GRA, shi kuwa Sarki Muhammadu Sanusi II na yin nasa harkokin ne a fadar sarkin Kano ta cikin gari.
Dandalin Mu Tattauna