Jami'in ma'aikatar lafiya da walwalar jama'a, Kachollum Daju, ya tabbatar da cewa wasikar da aka aikewa shugabanin asibitoci da manyan daraktocinsu wacce sakonta ya bayyana a baya-bayan nan, an aikata ne domin gargadi amma ba don tada hankalin al'umma ba.
A ci gaba da jawabinsa, Daju yace an gano kwayar cutar korona samfurin XEC a kasashe 29, kuma saboda karatowar lokacin bukukuwan karshen shekara, lokacin da matafiya za su zo daga sassan duniya daban-daban, yana da muhimmanci ga asibitoci su aiwatar da matakan da za su tabbatar ba a shammaci kasar ba.
A wata wasika mai dauke da kwanan wata 5 ga watan Disamban da muke ciki, ma'aikatar lafiya ta tarayyar Najeriya ta bukaci hukumomin lafiya su kaddamar da tsarin ko ta kwana a fadin asibitocinsu tare da sanya idanu sossai a kan marasa lafiya masu dauke da alamomin cutar korona.
Dandalin Mu Tattauna