Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Mulkin Sojin Burkina Faso Ta Kori Firaminista, Ministoci


Dokar ta soji ba ta bayyana wani dalili na korar Tambela ba, wanda aka nada matsayin firimiyan rikon kwarya jim kadan bayan Traore ya kwace mulki a watan Satumban shekara ta 2022.

Majalisar mulkin soji ta kasar Burkina Faso ta kori Firaministan rikon kwarya Apollinaire Joachim Kelem de Tambela, tare kuma da rusa gwamnatin kasar, a cewar wata sanarwar dokar da ofishin shugaban mulkin soji Ibrahim Traore ya fitar a jiya Juma'a.

Dokar ta soji ba ta bayyana wani dalili na korar Tambela ba, wanda aka nada matsayin firimiyan rikon kwarya jim kadan bayan Traore ya kwace mulki a watan Satumban shekara ta 2022, a daya daga cikin jerin juye-juyen mulkin da sojoji suka yi a yankin Sahel na yammacin Afirka da ke fama da rashin kwanciyar hankali a 'yan shekarun nan.

Firaiministan Burkina Faso, Apollinaire Joachim Kyelem de Tambela
Firaiministan Burkina Faso, Apollinaire Joachim Kyelem de Tambela

Dokar ta ce membobin gwamnatin da aka rusa za su ci gaba da gudanar da ayukansu har sai an nada sabuwar majalisar ministoci.

Kasar ta Burkina tana faman yaki da ‘yan tada kayar baya masu tsattsauran ra’ayin Islama, wasun su na da alaka da kungiyoyin al-Qaida da IS, tun bayan da suka bazu zuwa cikin kasarta daga makwabciyarta Mali kusan shekaru goma da suka gabata.

An kashe dubban 'yan kasar Burkina Faso a cikin 'yan shekarun nan a hare-haren 'yan bindiga, sannan kuma sama da mutane miliyan 2 sun rasa muhallansu, rabinsu kananan yara.

Ci gaban rikicin ya jefa dubun-dubatar 'yan kasar Burkina Faso cikin halin yunwa. Masu sharhi sun ce akalla rabin yankin kasar ta Burkina Faso har yanzu ba ya karkashin ikon gwamnati.

Traore ya sha alwashin yin abin da ya fi na magabatansa a lokacin da ya dare kan karagar mulki a shekarar 2022, amma lamarin tsaro ya kara tabarbarewa a karkashin gwamnatinsa, wadda kuma ta yi ta kokarin murkushe 'yan adawa, a cewar manazarta, da kungiyoyin kare hakkin bil adama da ma’aikatan jin kai.

Cire firaiministan na Burkina Faso na zuwa ne mako biyu bayan da a makwabciyar ta kuma abokiyar huldar ta Mali, sojojin da ke mulki suka tsige Firaiminista Dr Choguel Maiga daga mukaminsa tare da rusa gwamnatin da yake jagoranta bayan da ya zarge su da yin gaban kansu wajen gudanar da lamuran mulki.

Tuni aka maye gurbinsa da tsohon ministan ci gaban karkara Kanal Abdoulaye Maiga.

Choguel Maiga, Korarren Firaiministan Mali
Choguel Maiga, Korarren Firaiministan Mali

Maiga ya yi korafin cewa shugaban mulkin sojin kasar, Janar Assimi Goita da mukarrabansa ba sa shawara da shi wajen daukan muhimman matakan gudanar da lamuran mulki.

Tsohon firai ministan ya bada misalin yadda suka dage babban zaben kasar da ya kamata a gudanar a shekarar nan ta 2024 ba tare da tuntubar mambobin gwamnati ba.

A yayin gangamin kungiyoyi da jam’iyyu mambobin kawancen M5 RFP da ya jagoranta a karshen mako a Bamako ne firai ministan ya fallasa yanayin rashin shawarar da ake fama da shi a tafiyar gwamnatin rikon kwaryar kasar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG