Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Kama Wani Da Ake Zargi Da Safarar Makamai Daga Aljeriya Zuwa Najeriya


Bindigogi aka kama
Bindigogi aka kama

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta kama wani tsoho dan Jamhuriyar Nijar mai shekaru 58 da haihuwa da ake zargi da safarar makamai daga kasar Aljeriya zuwa Najeriya tare da kwato bindigogi kirar AK47 guda 16.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, CP Shehu Mohammad Dalijan wanda ya gabatar da wadanda ake zargi da aikata laifuffaka daban daban su 22 a hedikwatar ‘yan sanda, da ke Gusau a yau Talata ya ce wadanda ake zargin sun hada da wani mai kera bindigogi kirar AK 47 da kuma bindigogi kirar SMG wanda aka kamo daga jihar Filato.

Bindigogi kirar AK47
Bindigogi kirar AK47

Kwamishinan 'yan sandan ya ce rundunar ta kuma kama wasu da ake zargi da suka hada da masu samar da kayan aiki ga ‘yan bindiga wadanda aka kama su da tsabar kudi Naira miliyan biyu da dubu dari biyar a lokacin da suke hanyar zuwa kasuwa domin sayawa yan bindiga babur.

Kudi da aka kama
Kudi da aka kama

Ya kara da cewa sun kuma kama harsashai, da tabar wiwi da layoyi da sihiri daga hannun wadanda aka kama.

Bindigogi da aka kama
Bindigogi da aka kama

A cewarsa, sauran wadanda aka kama sun hada da masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, tare da kwato na’urorin hakar ma’adinai.

Dalijan ya bayyana cewa ‘yan sanda sun samu nasarar kama su a wasu sassan jihar Zamfara, Filato da Sokoto.

Ya ce sun yi aiki ne da sahihan bayanai da suka samu don cimma nasarar tare da yin kira ga mazauna yankin da su tallafawa hukumomin tsaro da muhimman bayanai.

Kwamishinan ya yi gargadin cewa gwamnatin tarayya da na jihar sun haramta hakar ma’adanai a fadin jihar don haka ya yi kira ga duk masu aikata wannan aika-aikar da su dakatar da yin hakan.

'Yan Sanda Sun Kama Wani Da Ake Zargi Da Safarar Makamai Daga Aljeriya Zuwa Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:54 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG