Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana cewar jiha za ta biya ma’aikatanta mafi karancin albashi na N85, 000, wanda ya dara n70, 000 da gwamnatin tarayyar Najeriya ta amince da ita a watan Yulin daNya gabata da n15, 000.
Sanwo-Olu, wanda ya kasance bako a shirin siyasar tashar talabijin ta Channels “Politics Today” na jiya Laraba, yace ba wai jihar za ta biya N85, 000 domin nuna fifiko akan sauran takwarorinta bane, a’a saidai domin tana da ikon yin hakan.
“Ina mai alfaharin shaida muku cewa, a yau mafi karancin albashin Legas da muka cimma matsaya tsakaninmu da kungiyoyi kwadagonmu shine N85, 000,” a cewar Sanwo-Olu a cikin shirin.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa a farkon shekarar da muke ciki ma saida jihar ta kara albashin ma’aikatanta, inda ya kara da cewa yana da burin mayar da mafi karancin albashin N100, 000 a watan janairun 2025.
“Zan so in dawo muku a watan Janairu da cewar mun iya kara mafi karancin albashin jihar Legas zuwa N100, 000 ba wai don in batawa kowa ba, sai don kaunar da nake da ita ga al’ummata su samu albashin daya dace, ina so su san cewar gwamnati nayi musu aiki,” a cewarsa.
A watan Yulin da ya gabata ne Shugaban Kasa Bola Tinubu ya rattaba hannu a kan kudirin dokar mafi karancin albashi na N70, 000, inda ya kawo karshen tattaunawar watanni tsakanin wakilan gwamnati da kungiyoyin kwadago dana kamfanoni masu zaman kansu.
Dandalin Mu Tattauna