Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Najeriya Miliyan 14 Sun Kara Talaucewa A Bana-Bankin Duniya


'Yan Najeriya a wajen gangamin siyasa
'Yan Najeriya a wajen gangamin siyasa

A cewar rahoton, an samu kari da mutum miliyan 115 a 2023 zuwa 129 a 2024, abinda ke nufin cewa ‘yan Najeriya miliyan 14 sun kara talaucewa a bana.

Bankin duniya ya saki rahoto a kan ci gaban Najeriya, inda yace fiye da ‘yan Najeriya milyan 129 ne ke cikin kangin talauci.

A jiya Alhamis ne bankin duniyan ya saki rahoton a daidai lokacin da hauhawar farashin gaba-dayan kayan bukatu ke kara tashi, abinda ke kara jefa miliyoyin ‘yan Najeriya cikin yunwa.

Kayan abinci
Kayan abinci

A cewar bankin, wannan adadi na fiye da ‘yan Najeriya miliyan 129 na wakiltar tashin gwauron zabo daga kaso 40.1 cikin 100 da aka gani a 2018 zuwa kaso 56 cikin 100 a bana.

An ruwaito rahoton na bankin duniyar na cewa, “sakamakon gazawar bunkasa wajen iya tserewa hauhawar farashi, talauci ya yi tashin gwauron zabo.

Tun a shekarar 2018, an kiyasta cewa adadin ‘yan Najeriya dake rayuwa cikin kangin talauci ya yi matukar karuwa da kaso 40.1 zuwa kaso 56 cikin 100.

Kayan abinci a kasuwar Najeriya
Kayan abinci a kasuwar Najeriya

“Idan aka hada da karuwar yawan jama’a, hakan na nufin cewar wasu ‘yan Najeriya miliyan 129 na rayuwa cikin talauci. Wannan karin na nuni da yadda bunkasar Najeriya ke cikin mawuyacin hali. Yanayin bunkasar tattalin arzikin Najeriya bai farfado zuwa mizanin da yake ba gabanin koma bayan arzikin da farashin mai ya sabbaba a 2016.

Aannobar korona ta sake ta’azzara koma bayan tattalin arzikin kasar.

A cewar rahoton, an samu kari da mutum miliyan 115 a 2023 zuwa 129 a 2024, abinda ke nufin cewa ‘yan Najeriya miliyan 14 sun kara talaucewa a bana.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG