‘Yan majalisar kasar Kenya sun kada kuri’ar ci gaba da shirin tsige mataimakin shugaban kasar Rigathi Gachagua, duk da yana fama da rashin lafiya.
Majalisar dattijai ta amince da tuhume-tuhume biyar daga cikin 11 da ake tuhumar Gachagua, inda nan take ta cire shi daga mukaminsa, kamar yadda kakakin majalisar dattawan Amason Kingi ya sanar da tsakar Alhamis.
Gachagua, wanda ya kamata ya ba da bahasi da kansa, an kwantar da shi a asibiti kan abin da lauyoyinsa suka bayyana a matsayin tsananin ciwon kirji kafin ya iya yin hakan.
An dakatar da zaman amma daga bisani aka ci gaba.
Gachagua shi ne mataimakin shugaban kasa na farko da aka taba tsigewa a tarihin Kenya.
A karshe ‘yan majalisar dattawan sun kada kuri’ar kan tuhume-tuhume 11 da suka hada zarge-zarge zagon kasa, mallakar dukiya ba bisa ka’ida ba, da yiwa shugaban kasa zagon kasa da dai sauransu.
Gachagua ya musanta dukkan tuhume-tuhumen.
Dandalin Mu Tattauna