Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliyar Ruwa: Gwamnati Ta Gargadi ‘Yan Najeriya, Akan Su Matsa Daga Gabar Koguna


Ambaliyar ruwa a Maiduguri
Ambaliyar ruwa a Maiduguri

Hakan na zuwa ne bayan da sakin ruwan da aka yi daga madatsar ruwa ta Alau ya hallaka fiye da mutane 30 tare da yin awon gaba da dubban gidaje a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Gwamnatin tarayyar Najeriya, ta hannun hukumar dake kula da kogunan kasar (NIHSA), ta shawarci al’ummomin dake zaune kusa da gabar kogin Benuwe da su gaggauta matsawa zuwa wuraren da basu da hatsari.

A sanarwar da ya fitar a yau Alhamis, babban daraktan NIHSA, Umar Muhammad, ya yi gargadin cewa yawan ruwan dake kogin Benuwe ya kai mizanin yin ambaliya saboda karuwar ruwan sama.

Haka kuma ya bukaci mazauna kusa da kogin Neja dasu matsa zuwa wuraren da basu da hatsari kasancewar hukumomin gudanarwar madatsun ruwan Kainji da Jebba na kokarin shawo kan ruwan daga yin ambaliya.

A baya-bayan nan, gwamnati ta gargadi ‘yan Najeriya da su matsa zuwa wuraren da basu da hatsari sakamakon sako ruwan da aka yi daga madatsar ruwa ta Lagdo a jamhuriyar Kamaru.

Hakan na zuwa ne bayan da sakin ruwan da aka yi daga madatsar ruwa ta Alau ya hallaka fiye da mutane 30 tare da yin awon gaba da dubban gidaje a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG