Majalisar Wakilan Najeriya ta shigo cikin batun karin farashin albarkatun man fetur din da aka yi a kasar.
Kudirin da Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye, Aliyu Madaki ya gabatar ya samu goyon bayan mambobin majalisar 111, inda ta bukaci a gaggauta janye karin farashin man fetur da gas din girkin da aka yi.
‘Yan majalisar sun bayyana fargabar da suke da ita na cewar karin na ta’azzara halin matsin rayuwa tare da yin barazana ga dorewar ayyukan ‘yan Najeriya.
Haka kuma majalisar ta bukaci kamfanin man fetur din Najeriya (nnpcl) da ma’aikatar albarkatun man fetur, su kara yawan man da ake tacewa a Najeriya, sannan suka bukaci babban bankin kasar (cbn) ya aiwatar da manufofin kudin da zasu takaita tasirin karin farashin man akan hauhawar farashin kayan masarufi.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da bankin duniya ke gargadin cewar cigaba da karin farashin man fetur na iya dawo da radadin janye tallafin man fetur daya fara raguwa sabo a Najeriya.
Gargadin na kunshe ne a cikin rahoton mujallar “Africa Pulse” na watan Oktoba.
Dandalin Mu Tattauna