Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiragen Yakin Najeriya Na Ci Gaba Da Luguden Wuta Akan Sansanonin Boko Haram


Jirgin Sama Na Yakin Sojojin Najeriya
Jirgin Sama Na Yakin Sojojin Najeriya

Jiragen yakin Najeriya sun sami nasarar auna mabuyar ‘yan ta'addar Boko Haram a zirin tafkin Chadi, yankunan Tumbun Fulani da Tumbun Shitu inda ake ganin na zama barazana ga cibiyoyin soji da ma al'ummar yankunan.

ABUJA, NIGERIA - Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwar da daraktan labaru da hulda da jama'a na hedkwatar mayakan saman, Air Commodore Edward Gabkwet ya sanya hanu a kai ranar Litinin.

Tunda farko dai an lura yan ta'addan na loda jarkokin mai a wasu motocin yaki na ‘yan ta'addar a wurin da aka yi amanna babbar cibiyar ajiyar kayayyakin ‘yan ta'addan ne.

Wannan ya sa aka ta da jiragen yaki wadanda suka yi ruwan wuta a wadannan sansanoni kuma suka kone wuraren kurmus tare da hallaka ‘yan ta'addan da ke wurin da kuma lalata motocin da aka girke masu manyan bindigogin harbo jiragen sama.

Jiragen yakin kazalika sun kuma hango wasu motocin a kori-kura dauke da manyan makamai da mayaka na nufowa wurin, inda nan take suma aka harba masu bama-bamai aka tarwatsa su.

Sojojin Najeriyar sun kara nanata kudirinsu na ci gaba da tabbatar da tsaro ne a Arewa maso Gabas da ma sauran sassan Najeriya daban-daban.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG