Kwamitin bincike da majalisar dokokin jihar Plato ta kafa domin gano masababin tashe tashen hankali da ake fama da shi tsakanin Fulani da Manoma a jihar ya gano cewa, dukan bangarorin dake kai ruwa rana suna da manyan makamai
Gwamnatin jihar Kano ta sallami ma’aikatan wucin gadi dubu biyu da dari shida da ishirin bayan sun kwashe shekaru takwas suna aiki a hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar, sai dai kungiyar kwadago ta najeriya reshen jihar Kano ta kalubalanci matakin.
Wadansu gwamnatocin Najeriya sun bi sahun jihohin Kaduna da Nassarawa wajen bayyana niyar janye daukar nauyin zuwa ayyukan ibada na Musulmi da Kirista.
Hukumar hana fasakauri, kwastan a Nigeria ta kona naman kajin turawa na kimamin fiye da naira miliyan daya, da aka shigo da su ba bisa ka'idar doka ba.
Kungiyoyin yaki da cin hanci da rashawa a Nigeria sun baiyana bukatar a ruguza daukaucin kamfanin kula da harkokin mai na kasa NNPC
Zarge zargen cin hancin naira miliyan 15 ya dabaibaiye shar'ar zaben gwamnan jihar Yobe, arewa maso gabashin Nigeria da ake yi a birnin Abuja
Wakilan Majalisar Dokokin Nigeria sun bada tabbacin ganin bayan tarzomar 'yan Boko Haram.
Jami'ar Bayero dake Kano ta kafa wata sabuwar cibiya ta nazarin habaka bincike da bada horo kan al'arran tattalin arziki da zamantakewa.
Kwana daya bayan da shugaban Nigeria Mohammadu Buhari ya nada sabon shugaba a ma'aikatar mai ta Nigeria, an ci gaba da yin garambawul a ma'aikatar.
Kungiyar masu Canjin kudaden kasashen ketare sun koka game da sabbin matakan hada hadan kudaden kasashen waje da Babban Bankin Kasa na CBN ya fitar
Ambaliyar ruwa a jihar Yobe ta yi sanadiyar mutuwar wata yarinya yar shekara biyu
Majalisar dattijan Nigeria ta tantance manyan hafsoshin hukumomin tsaro bayan sa'o'i biyar tana yi musu tambayoyi
Domin Kari