Wakilan Majalisar Dokokin Nigeria sun bada tabbacin ganin bayan tarzomar 'yan Boko Haram.
Jami'ar Bayero dake Kano ta kafa wata sabuwar cibiya ta nazarin habaka bincike da bada horo kan al'arran tattalin arziki da zamantakewa.
Kwana daya bayan da shugaban Nigeria Mohammadu Buhari ya nada sabon shugaba a ma'aikatar mai ta Nigeria, an ci gaba da yin garambawul a ma'aikatar.
Kungiyar masu Canjin kudaden kasashen ketare sun koka game da sabbin matakan hada hadan kudaden kasashen waje da Babban Bankin Kasa na CBN ya fitar
Ambaliyar ruwa a jihar Yobe ta yi sanadiyar mutuwar wata yarinya yar shekara biyu
Majalisar dattijan Nigeria ta tantance manyan hafsoshin hukumomin tsaro bayan sa'o'i biyar tana yi musu tambayoyi
Duk da kwarmaton da ma’aikata suka rika yi kafin gwamnati ta biyasu albashin watan da ya gabata, gwamnan jihar Kaduna Nasiru el-Rufa’I yace wannan watan ma sai an tantance ma’aikata kafin a biyasu albashin nasu.
Gwammnatin jihar Borno ta fara kwashe ‘yan gudun hijira daga jihar da kasar Kamaru ta tasa kyeyarsu . sama da ‘yan gudun hijira dubu biyu ne aka tasa keyarsu zuwa Najeriya bayan sun ketara kasar Kamaru domin gujewa hare haren kungiyar Boko Haram.
Kungiyar tsofaffin ‘yan sanda a Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya da ta duba tsarin biyan kudin sallama da fenshon ‘ya‘yanta domin su sami rayuwa mai inganci.
Rundunar yan sandan jihar Oyo ta kama wasu barayi matasa masu satar mutane, da suka sace wani dattijo.
Rundunar sojan Nigeria, shiya ta bakwai dake birnin Maiduguri, arewa maso gabashin Nigeria ta samu nasarar lalata sansanonin yan Boko Haram a karamar hukumar Konduga
Shugaba Buhari yayi la’akari da kyakyar dangantakar dake tsakanin Nigeria da Kamaru, a saboda haka yace tilas kasashen biyu sun hada kai wajen yaki da yan Boko Haram
Domin Kari