Rahotanin dake fitowa daga jihar Yobe na cewa an samu ambaliyar ruwa harma ta yi sanadiyar mutuwar wata yarinya yar shekara 2.
Ambaliyar ruwar ta apku ne a sakamakon ruwan saman da aka yi ta tapkawa kamar da bakin kwarya. Ambaliyar ta rushe gidaje da dama da kashe wasu dabbobi.
Mallam Chiroma Buba dan Majalisar dake wakiltar mazabar Jajere ya shedawa wakilin sashen Hausa Haruna Dauda Biu cewa tuni dama mutane ke fama da matsalar rashin tsaro. Mutane basu samu damar yin noma ba, sai kuma aka wayi gari, gidan da mutum yake zaune a cikin ta ambaliyar ruwa ta rushe
Yaya ke nan.
A jihar Kano batun karyewar gadoji da lalacewar hanyoyin mota musamman a yankunan karkara a sakamakon yawan ruwan sama da ake samu a 'yan kwanakin nan, ya haifar da kunci ga rayuwar jama'a a wasu kananan hukumomin jihar.
Mazauna karamar hukumar Warawa sun fadawa wakilin sashen Hausa Mahmud Ibrahim Kwari cewa, motoci da babura sai kafewa suke sai an fiddo su.
A kauyen Jimagu ma bata canja zani ba. Mazauna kauyen suka ce idan aka yi ruwa, ba fita ba kuma shiga. Mazauna kauyen sunce suna bukatar hukumomi su kai musu dauki.