Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wakilan Majalisar Dokokin Nigeria sun yi alkawarin kawo karshen tarzoma


Ginin Majalisar taraiyar Nigeria
Ginin Majalisar taraiyar Nigeria

Wakilan Majalisar Dokokin Nigeria sun bada tabbacin ganin bayan tarzomar 'yan Boko Haram.

Wakilan Majalisar dokokin Nigeria sun bada tabbacin daukan dukkan mataka daya kamata na ganin bayan tarzomar yan Boko Haram.

Wakilan sun bada wannan tabbacin ne a lokacinda suka je nazarin irin barnar da yan Boko Haram suka yi a jihar Adamawa.

Wakilin sashen Hausa Ibrahim Abdulaziz ya aiko da rahoton cewa mataimakin shugaban Majalisar Dattijai Ekweremadu shine ya jagoranci tawagar.

Senata Ali Ndume, daga mazabar jihar Borno yana daya daga cikin wakilan, da suka kai wannan ziyara. Yace zasu taimaka ta kowace fuska na ganin an tallafawa wadanda rikicin Boko Haram ya shafa. Ya bada tabbacin cewa a matsayinsu na wakilan Majalisar dattijai, zasu bada hadin kai ga yunkurin da shugaba Buhari ya ke yi na kawo karshen wannan matsala.

Yace ciwo ne wanda ada kadan ne, yanzu kuma ya yadu, ya zama abinda duk duniya sun damu da ita. Yace sai gashi kuma sabon shugaban Nigeria yana baiwa batun matakan tsaro a arewa maso gabashin Nigeria fifiko.

A saboda haka yace hakki ne akan yan Majalisa su tabbatar da cewa sun yi duk abinda ya kamata su yi, na bada goyon baya da baiwa gwamnatin karfin gwiwa don a tabbata samun nasarar abinda aka sa a gaba.

Senata Ali Ndume yace ba wai kawai zasu zauna a Abuja suna ta surutai kawai ba. Ya kamata su je duk inda al'amari yafi kamari su gani da idanuwansu abubuwan da suke faruwa, kuma suyi shawarwari da jamaan yankunan domin sanin irin taimakon da suke so daga wajen gwamnati.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00

XS
SM
MD
LG