Shugaba Barack Obama na Amirka yace yarjejeniyar da aka kula da Iran akan shirin nukiliyarta zata toshe mata duk wata kafar da take da shi na kera bam din atam. Shugaba Obama yayi wannan furucin ne a lokacinda yake maida martani ga damuwar da Yahudawan Amirka suka nuna akan yarjejeniyar.
Baban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Banki Moon yace rashin ya baci sosai da ya ji labarin cewa an gano gawarwarkin yan gudun hijira saba'in da daya cikin wata babar mota akan wata babar hanya a kasar Austria kusa da kan iyakar kasar Hungary.
Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya yace a shirye yake ya azawa bangarorin kasar Sudan ta kudu takunkumi, idan basu kaddamar da sabuwar yarjejeniyar samun zaman lafiya kacokan dinta ba.
An tabbatar da mutuwar mutane goma sha daya a wani hadarin jirgin kwale kwale a jihar Niger
Jami'an tsaro sun ce suna ci gaba da binciken dalilin rasuwar mataimakin gwamnan jihar Borno Zannah Umar Mustapha a Yola kwanakin baya
Yau Kungiyar Malaman Sabuwar Jami’ar koyon aikin malanta ta Kano zata fara yajin aikin gargadi na mako guda,domin nuna bacin ransu game da matakin gwamnatin tarayya na soke Jami’ar tare da takwarrorinta dake Zaria da Owerri da kuma Ondo, da mayar dasu matsayinsu na baya wato kwalejojin ilimi.
Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya kalubalanci gwamnonin Najeriya su yi amfani da manufofin muradun karni masu dorewa
Mai Martaba Sarkin Musulmi Sa’ad Abbubakar da Mai alfarma Sarkin Kano Sanusi na biyu sun kaddamar da jigilar alhazan bana.
A ranar Asabar dubban 'yan gudun hijira suka bi ta kan yan sandan kasar Macedonia wadanda suke dauke da kulake. Yan sandan sun yi kokarin hana yan gudun hijira shiga kasar daga kasar Girka
Wani hari da aka kai Kabul baban birnin kasar Afghanistan ya kashe mutane goma sha biyu, ciki harda wasu 'yan kwangila wadanda suke yiwa kungiyar kawancen tsaro ta NATO aiki a kasar
An kashe akalla mutane 18 a hare haren bama bamai guda biyu dabam dabam da yan kungiyar Al Shabab suka kai a kasar Somaliya
Jiya Juma'a wani dan bindiga ya bude wuta akn wani jirgin kasa dake tafiya tsakanin birnin Armsterdan na kasar Holland ko Netherlands zai birnin Paris na kasar Faransa,
Domin Kari