An tabbatar da mutuwar mutane goma sha daya a wani hadarin jirgin kwale kwale a jihar Niger
Jami'an tsaro sun ce suna ci gaba da binciken dalilin rasuwar mataimakin gwamnan jihar Borno Zannah Umar Mustapha a Yola kwanakin baya
Yau Kungiyar Malaman Sabuwar Jami’ar koyon aikin malanta ta Kano zata fara yajin aikin gargadi na mako guda,domin nuna bacin ransu game da matakin gwamnatin tarayya na soke Jami’ar tare da takwarrorinta dake Zaria da Owerri da kuma Ondo, da mayar dasu matsayinsu na baya wato kwalejojin ilimi.
Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya kalubalanci gwamnonin Najeriya su yi amfani da manufofin muradun karni masu dorewa
Mai Martaba Sarkin Musulmi Sa’ad Abbubakar da Mai alfarma Sarkin Kano Sanusi na biyu sun kaddamar da jigilar alhazan bana.
A ranar Asabar dubban 'yan gudun hijira suka bi ta kan yan sandan kasar Macedonia wadanda suke dauke da kulake. Yan sandan sun yi kokarin hana yan gudun hijira shiga kasar daga kasar Girka
Wani hari da aka kai Kabul baban birnin kasar Afghanistan ya kashe mutane goma sha biyu, ciki harda wasu 'yan kwangila wadanda suke yiwa kungiyar kawancen tsaro ta NATO aiki a kasar
An kashe akalla mutane 18 a hare haren bama bamai guda biyu dabam dabam da yan kungiyar Al Shabab suka kai a kasar Somaliya
Jiya Juma'a wani dan bindiga ya bude wuta akn wani jirgin kasa dake tafiya tsakanin birnin Armsterdan na kasar Holland ko Netherlands zai birnin Paris na kasar Faransa,
Tsoron da ake nunawa akan tafiyar hawaniyar da bunkasar tattalin arzikin China ke yi da rashin sanin tabbas akan harkokin siyasar kasar Girka da kuma rashin sanin tabbas akan shirye shiryen da ake yi ba kara kudi ruwa da hukumomin Amurka suke tunanin yi sun girgiza masu zuba jarri,.
Ranar Lahadi idan Allah ya kaimu aka shirya, baban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Banki Moon zai kai ziyara Nigeria domin ganawa da sabon shugaban kasar Muhammdu Buhari da kuma tunawa da mumunar harin da aka kaiwa ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Abuja a shekara ta dubu biyu da goma sha daya.
Iran ta baiwa hukumar makamashin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya da ake cewa IAEA a takaice takardun da aka danganta da zarge zargen da ake yi mata cewa tayi ko kuma tana kokarin kera makaman atom.
Domin Kari