Kasar Kamaru ta fara maido yan Nigeria wadanda suke gudun hijira a kasar, Wadanda suka fara isowa ta yankin Mubi jihar Adamawa jami'an tsaro sun tantance su kafin hukumomin agaji su karbe su.
Ziyarar da shugaba Barack Obama na Amirka zai kai kasar Kenya tamkar haske ne akan kasar ta kuma salon gwamnatin shugaba Uhuru Kenyatta
Yajin aikin rukunoni Likitoci masu neman kwarewa a fannoni dabam dabam a Nigeria, yana ci gaba da gurgunta harkokin kiwon lafiya a kasar
Wasu da ake zaton yan kungiyar Boko Haram ne, sun kai hari garin Miringa, a jihar Bornoi suka kashe mutane takwas a ranar Laraba da dare
Shugaba Muhamdu Buhari na Nigeria yace rundunar hadin gwiwa na yaki da yan kungiyar Boko Haram zata fara aiki a karshen watan Yuli idan Allah ya yarda.
Shugaba Muamadu Buhari ya bukaci yan kasuwa da su taimaka wajen habaka tattalin arzikin Nigeria
Tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya ce haka rayuwa take. Tsohon gwamnan ya yi wannan furuci ne a wata hira da sashen Hausa na Muryar Amirka, ya yi da shi bayan wata kotu ta ba da belinsa.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar ya kalubalanci illahirin al’ummar Najeriya musamman shugabannin hafsoshin sojin kasar da shugaba Muhammadu Buhari ya nada, dangane da yanayin tsaro da kasar ke ciki a halin yanzu.
Kotu ta bada belin tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido, Yayinda ake jiran cika sharuddan belin 'ya'yansa biyu da aka tsare su tare.
Mallam addini a jihar Plato sun bukaci al’umma su hada kai ba tare da nuna banbanci ba, wajen bankado bata gari dake hallaka rayuwan al’umma da basu ci ba basu gani ba.
Gwamnatin kasar Jamus, da kuma jihohin Oyo da Kano a Najeriya, sun fara wani shiri da zai sanya ido a game da barkewar cututuka, tare da daukar matakin gaggawa na shawo kansu.
Domin Kari