A cewar shugaban kwamitin kuma mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Plato,Yusuf Adamu Gardi, kwamitin ya fara aiki kuma ya fahimci cewa, dalilin tashin hankalin nan akan wurin kiwo ne, inda shanu zasu yi kiwo a wurinda bai makata su yi kiwo ba.
Yace akwai wurare-gandun daji-da aka kebe inda aka haramtawa Fulani yin kiwo, wadanda ba a kiwo a lokutan baya, amma yau Fulani suna shiga suyi kiwo, akwai kuma gonakin kabilar Berom da bai kamata a bari dabbobi su shiga ba, wadansu Fulani suna bari dabbobinsu su shiga suyi masu barna.
Haka kuma, zaka tarar wadansu ‘yan kabilar Berom sun kebe wuraren da dabbobi suke wucewa-labi-labi- suna noma a wurin su hana shanu wucewa, yayinda Fulani kuma har wa yau suke barin shanu su shiga lambun Berom suyi masu barna. Wannan yasa ake samun tashe tashen hankali tsakanin manoma da makiyaya kasancewa dukan bangarorin suna da makamai.
Mataimakin kakakin majalisar dokokin yace, bincikensu ya nuna cewa, akwai bindigogi a hannun mutane da yawa, kuma duk inda aka samu makamai da yawa a hannun mutanen da bai kamata ba, za a sami tashin hankali. Dalili ke nan da yace, suna neman shugabannin al’ummomin domin neman hadin kai da goyon bayansu a yunkurinsu na neman ganin an sami zaman lafiya mai dorewa.
Ga cikakken rahoton da wakiliyar sashen Hausa Zainab Babaji ta aiko daga Jos,Najeriya.