Jami'ar Bayero dake Kano ta kafa wata sabuwar cibiya ta nazarin habaka bincike da bada horo kan alamurran tattalin arziki da zamantakewa da kuma kimiyar kididdigar Jama'a.
Wakilin sashen Hausa Mahmud Ibrahim Kwari ya aiko da rahoton cewa cibiyar wadda hukumar gudanarwa ta amince da kafuwarta kwanakin baya, ta kunshi nazari da bincike a kusan dukkan farnonin na rayuwar Bil Adama.
Wadannan farnonin kuwa sun hada harda na tattalin arziki da aiyukan noma da kiwon lafiyar jama'a da zamantakewa da siyasa da kuma kimiyar kididdigar jama'a.
A ranar Talata kwamitin da aka dorwa alhakin tsara yadda aiyukan cibiyar zasu gudana, ya shirya wani taron masu ruwa da tsaki a harabar jami'ar Bayero.
Farsesa Isma'ila Zango na sashen nazain zamantakewar dan Adama a jami'ar shine shugaban kwamitin. Yace zai fi kyau kafin cibiyar ta fara aiki a tattaro masana daga bangarori dabam dabam da kuma wadanda suka jibanci harkokin wadannan abubuwa da kuma sauran jama'a na gari, suma su zo su ga, shin cibiyar nan wane irin abu ko kuma abubuwa cibiyar zata fi maida hakali akai.
Farfesa Garba wani kwararai kan nazarin tattalin arziki kuma Malami a jami'ar. Yace ta bangaren tattalin arziki suna fatar cibiyar zata fito da hanyoyi ayi bincike, kuma ya kasance kamar yadda ake samu a kasashen waje, ayi bincike ba a yar da shi ba. Kuma a samu maso goyon bayan binciken, wadanda zasu sa jarinsu ko wani abu, kamar dai yadda turawa su ke yi.
Shi kuma farfesa Saidu Ahmed Dukawa masanin kimiyar siyasa, cewa yayi akwai hanyoyin da irin wadannan cibiyoyi ya kamata su bi har akai ga cimma nasara. Domin kada a samu karancin kudaden gudanar da nazarin bincike. Da kuma kaucewa gazawar shugabanin gwamnati wajen yin aiki da illimin dake kunshe cikin sakamakon binciken.