Bayan data kwashe sa'o'i biyar tana yiwa shugabanin hukumomin tsaron Nigeria tambayoyi, Majalisar dattijan Nigeria ta tantance kuma ta amince da nadin su.
Shugaban Majalisar Dattijai Senata Bukola Saraki shine ya tabbatar da nadin nasu bayan da aka gama yi musu tambayoyi.
Senata Abu Ibrahim yace dukkan su an yaba musu, sunyi abinda ya kamata kuma sun nuna suna da illimi da goguwa ko kuma kwarewar rike mukaman da aka basu
Shi kuwa Senata Kabiru Gaya yace sun kwashe sa'o'i biyar suna yiwa shugabanin hukumomin tsaro tambayoyi domin tantance su a saboda wahalar da Nigeria ta shiga. Yace a baya wasu sojoji sunce rundunar sojan Nigeria tana fama karancin makamai.
Wasu sojojin kuma sunce ba'a biyan su yadda ya kamata ko kuma sam sam ba'a biyan su alawus din su. Dalilan da suka sa ke nan aka dauki tsawon lokaci wajen tantance su, to amma senata Gaya yace sun gamsu
A watan jiya na Yuli shugaba Muhammadu Buhari ya nada su, bayan daya sauke wadanda ya gada daga tsoguwar gwamnatin Jonathan.