Rundunar sojin da ke aikin wanzar da zaman lafiya a jihar ta ce ta kama mutum 12 da take zargi da hannu a kisan matafiyan.
Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta ce ta gano wasu shugabanni da aka ba su beli ake kuma mika yatsa a kansu kan hare-haren da aka yi a wasu sassan arewacin jihar.
An kashe mutane da dama a wani rikici tsakanin Irigwe da Fulani a karamar hukumar Bassa da ke jihar Filato.
Kiristocin Najeriya masu ziyara sun tashi a karon farko zuwa kasar Jordan don gudanar da ayyukan ibada tun bayan barkewar Annobar COVID-19.
Majalisar dake sasanta tsakanin addinai a jihar Filato, ta kalubalanci jami’an tsaro da su gaggauta gano wadanda ke shigar-burtu da kakin soja ko na ‘yan sanda suna hallaka mutane.
Kai wa juna hare-haren ramukon gayya tsakanin Fulani makiyaya da manoma a kananan hukumomin arewacin jihar Filato, ya kasance abin da ke haifar da barazana ga zaman lafiya a yankin.
Kungiyar kwadago a Jihar Nasarawa da ke tsakiyar arewacin Najeriya ta kasa cimma matsaya da gwamnatin Jihar kan yarjejeniya da zai kawo karshen yajin aiki da ma’aikatan Jihar ke yi.
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya ki amincewa ya sanya hannu kan yarjejeniya da kungiyar kwadago dake yajin aiki saboda janyewa da gamayyar kungiyoyin ma’aikatan jinya a jihar ta yi daga yarjejeniyar.
A karshen makon jiya ne wa’adin mulkin shugabannin kananan hukumomin jahar Nasarawa ya kare suka kuma mika mulki wa daraktocin ma’aikatan kananan hukumomi goma sha uku na jahar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato, ASP Gabriel Uba, ya tabbatar da mutuwar mutum bakwai ne a yankin na Dong inda ya ce ba su kama kowa ba amma suna kan gudanar da bincike.
Matasa daga sassa daban daban na Najeriya sun gudanar da gangamin karbar mulki daga hannun dattawa.
Majalisar addinai ta jihar Filato ta ce za ta dauki matakan tattaunawa a matsayin hanya mai kyau ta zaman lafiya tsakanin mabiya addinai daban-daban a jihar.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za ta samar da kayan aiki don tabbatar da duk wani dan Najeriya ya sami rigakafin COVID.
Jihar Filato da ke tsakiyar arewacin Najeriya, ta sha fama da rigingimu masu nasaba da addini da kabilanci.
Kungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya tace za ta baiwa sabbin shugabannan tsaro goyon baya don kawo karshen ayyukan ta’addanci a Najeriya
Ganin yadda matsalar tsaro ke kara ta’azzara a Najeriya, al’ummar da ke hankoron zaman lafiya da samun ci gaba na kara nemo hanyoyin da suka dace wajen cimma burinsu.
Mata a jihar Plato sun jaddada bukatar cika alkawarin da aka dauka na basu kashi talatin cikin dari na makaman siyasa, yayin da su ke bukin ranar mata ta duniya.
Kalaman gwamnan jihar Benue mai cewa fadar shugaban kasa na rikon sakainar kashi kan irin kashe-kashen da ake zargin Fulani makiyaya da aikatawa a sassa daban-daban na Najeriya, ya janyo kakkausan martani daga wasu kungiyoyi dake hankoron samar da ci gaban Najeriya.
Gwamnatin Jihar Benue ta ce ta dauki matakan shawo kan karuwar wadanda ke kamuwa da cutar kwalara a jihar, lamarin da ya yi sanadiyar rasa rayuka, musamman yara kanana.
Biyo bayan wata sanarwa da hukumar tsaron farin kaya ta DSS a Najeriya ta fitar inda ta ce ta bankado wani shiri da wasu mutane ke yi na ingiza rikicin addini a kasar, jama’a sun fara tofa albarkacin bakinsu kan wannan batun.
Domin Kari