Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mata Suna Neman Gwamanati Ta Dama Da Su


Ranar Mata Ta Duniya 2021
Ranar Mata Ta Duniya 2021

Mata a jihar Plato sun jaddada bukatar cika alkawarin da aka dauka na basu kashi talatin cikin dari na makaman siyasa, yayin da su ke bukin ranar mata ta duniya.

Kamar kowace ranar takwas ga watan Maris, mata a fadin duniya kan fito don furta albarkacin bakinsu kan batutuwan da suka masu tarnaki suke kuma bukatar a magance su don inganta rayuwarsu, dalilin da ya sa matan na jihar suka bukaci gwamnati da ta cika alkawarin da ta masu.

Rana ce da mata sukan bayanna jin dadinsu da wasu nasarorin da saka samu a fannoni dabam-dabam na rayuwa.

Wadansu mata da Muryar Amurka ta tattauna da su sun ce suna alfahari da wannan rana, da suka ce tana jan hankalin al'umma wajen sanin kalubale da su ke fuskanta, a wadansu lokuta kuma gwamnatoci su kan dauki matakai na magance su. Wasu kuma sun nuna damuwarsu akan rashin ilmi da kuma babbancin da ake nuna wa tsakanin mata da maza a hakar karatu.

Matan sun ce dole ne a basu guraben shugabanci kafin a samu karshen wasu matsalolin da suke fuskanta.

A nashi bayanin, gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule yace suna kan kwazon tallafawa mata don dogara da kansu da kuma kula da iyalensu. Ya ce sun dauki matakai kamar na bada jari da wasu hanyoyin karfafawa mata.

Majalisar dinkin duniya ce dai ta ware ranar don ba mata su fadi matsalolinsu don samun waraka.

Saurari rahoton Zainab Babaji cikin sauti:

Mata Suna Neman Gwamanati Ta Dama Da Su
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00


XS
SM
MD
LG