Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abin Da ‘Yan Najeriya Ke Cewa Kan Batun Shirin Haddasa Rikicin Addini


Wasu sojoji Najeriya a bakin aiki.
Wasu sojoji Najeriya a bakin aiki.

Biyo bayan wata sanarwa da hukumar tsaron farin kaya ta DSS a Najeriya ta fitar inda ta ce ta bankado wani shiri da wasu mutane ke yi na ingiza rikicin addini a kasar, jama’a sun fara tofa albarkacin bakinsu kan wannan batun.

Mai magana da yawun kungiyar Jama’atu Nas’ril Islam a jihar Pilato. Malam Sani Mudi ya yaba da fadakarwar ta hukumar DSS ya kuma hori ‘yan Najeriya da su sanya kishin kasa a zukatansu.

“Mun gamsu idan aka duba abin da ake yi na rubuce-rubuce da yunkurin da akan yi da dama, kankanin abu sai ka ga an mayar da shin a addini.” In ji Sani Mudi.

Ya kara da cewa, “in ka ga abu na gyara, ka fade shi da kyayyawar niyya.”

Farfesa Yusufu Turaki, daya daga dattawan Najeriya da ya ba da gudunmowa wajen yin garanbawul a kundin tsarin mulkin Najeriya ya ce wadanda ke da hakkin tsaro ba su dauki harama ba.

“A Najeriya yau, wadannan mutane, ‘yan sanda da soja, ba su da niyyar su magance wahalhalun tsaro….wadanda ke rike da manyan mukamai a gwamnati, ba su da kaunar ‘yan Najeriya, ba bu ko kadan.” Farfesa Turaki ya ce.

Tsohon jami’in ‘yan sanda kuma tsohon kwamishina a jihar Pilato, Alhaji Abubakar Dashe, ya ce Najeriya na bukatar karin jami’an ‘yan sanda don tsaron kasar.

“’Yan sanda sun kasa gaba daya ko ina a Najeriya.” Dashe ya ce.

Wani mai fashin baki, Mr. Kicime Gwatau ya ce DSS ta yi namijin kokari wajen gano bata garin da ke neman haddasa rikici.

“Muna maraba da irin wannan mataki da suka dauka, sai dai kuma DSS tana da aikin yi.” Gwatau ya ce.

A farkon makon nan ne, hukumar ta DSS ta fitar da sanarawa cewa, ta bankado wata makarkashiya da wasu ke kullawa ta kokarin ta da rikicin addini a wasu jihohin Najeriya.

Hukumar ta lissafo jihohin Pilato, Sokoto, Kano, Rivers, Legas, Kaduna, Oyo da sauransu a matsayin wuraren da ake so a ingiza rikicin na addini.

Karin bayani akan: DSS​, jihar Pilato, Nigeria, da Najeriya.

XS
SM
MD
LG