Kwamishiniyar yada labarai, raya al’adu da yawon shakatawa ta jihar Benue, Madam Ngunan Adingi, ta ce gwamnatin jihar ta tura kwararrun likitoci a yankunan da cutar ta bulla.
Ta kara da cewa barkewar cutar ta fi shafar yankunan da ke kusa da ruwa ne, kuma yawancin wadanda cutar ta shafa yara ne. Gwmanatin jihar ta bada tallafin kudi da aka yi amfani da su wajen sayen sinadirin da ke tace ruwa tare da tura likatan yara don kula da marasa lafiya.
Dakta Samuel Audu, Darakta a ma’aikatar lafiya ta jihar Filato, ya ce rashin tsabtace muhalli, ruwan sha da abinci ke yada cutar.
Shi ma Dakta Shu’aibu Joga Dass, ya ce jama’a su rika wanke hannu da duk wani kayan marmari kafin su ci, don takaita yaduwar cutar ta kwalara.
Saurari cikaken rahoton Zainab Babaji cikin sauti: