Shugaban kungiyar kuma gwamnan jahar Pilato, Simon Lalong yace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umurnin samo jiragen da zasu taimaka wajen dakile matsalar tsaro a kasar.
Matakin na zuwa ne a dai dai lokacin da gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, yace wasu ‘yan bindiga sun kai masa hari a ranar Asabar, amma ya tsallake rijiya da baya.
ba-za-mu-amince-da-kai-hari-akan-dayanmu-ba---gwamnonin-najeriya
yan-bindiga-sun-kai-wa-gwamnan-benue-samuel-ortom-hari
Kwamishinar yada labarai da yawon shakatawa a jahar Binuwai, Madam Ngunan Adingi tace tuni gwamnan jihar ya rubuta takardar koke ga shugaban kasa.
A bangare guda kuwa kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, da gwamna Ortom ya bukaci a kame shugabannan ta bisa zargin kokarin hallaka shi, ta maida martani ta bakin shugabanta, Alhaji Bello Bodejo wanda yace basu da wata masaniya kan harin.
Karin bayani akan: Shugaba Muhammadu Buhari, jihar Benue, Samuel Ortom, Nigeria, da Najeriya.
A hirar shi da Muryar Amurka, Bello Bodejo ya ce Kungiyar Miyellti Allah Kautal Hore, ba kungiyar ta'addanci ba ce. Bisa ga cewarshi, gwamna Ortom ya zargi kungiyar da ta'addanci tun lokacin da ya kafa doka, su ka kuma nemi tattaunawa da shi sabili da bisa ga cewarshi, ba bu adalci a dokar sabili da babu wurin da aka ce Fulani ba za su iya cin moriya ba. Bodejo ya ce wannan zargi ne sabili da haka babu hannun kungiyar su a cikin lamarin.
Saurari rahoton Zainab Babaji cikin sauti: