A wani jawabi da ya yi wa manema labarai, gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bukaci gwamanatin tarayya da ta fito fili ta kalubalanci, tare kuma da kama, makiyayan dake daukar bindigogi kirar AK47.
Sai dai wasu kungiyoyi uku masu goyon bayan shugaban kasa, Muhammadu Buhari, sun maida martani kan kalaman na Ortom, ta hanyar fitar da wata takardar hadin gwiwa, inda suka bayyana shugaba Buhari a matsayin mutum na gari dake yin adalci ga kowa.
Shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta kasa, Muhammadu Kiruwa ya ce irin abubuwan da ake wa Fulani a kasar sun wuce hankalin mutum guda. Idan ana tuhumar mutum da aikata laifi bincike ya Kamata a gudanar ba wai kira da a kama mutum ba.
Mai fashin baki kan lamura, Yakubu Gidado ya ce samun adalan shugabanni ne kawai zai kawo karshe rashin tsaro da Najeriya ke fuskanta.
Domin cikakken bayani saurari rahotan Zainab Babaji.
Karin bayani akan: Jihar Benue, Samuel Ortom, Nigeria, da Najeriya.