Majalisar sasanta tsakanin addinai a jahar Pilato tace tana dab da bullo da matakan da take da yakinin zasu kawo karshen wasu rikice-rikice dake aukuwa da ake kuma dangantasu da addini.
Mai martaba Sarkin Wase kuma daya daga shugabannan majalisar, Alhaji Muhammadu Sambo Haruna yace zasu yi amfani da damar da gwamnati ta basu don samarda zaman lafiya da raba rikici da addini.
Tsohon shugaban darikar COCIN Rabaran Pandang Yamsat wanda shima shugaban majalisar ne yace burinsu shine su samar da hanyoyin zaman lafiya mai dorewa.
A halin da ake ciki kuma, rundunar ‘yan sandan jahar Binuwai tace ta fara gudanar da bincike don gano dalibai uku, na jami’ar harkokin noma dake garin Makurdi, da ‘yan bindiga suka yi garkuwa dasu.
Saurare cikakken rahoton Zainab Babaji cikin sauti: