Hukumar kula da masu ziyara zuwa kasa mai tsarki ta mabiya addinin Kirista ta ce masu ziyara 2,500 ne za su ziyarci kasar Urdun wato Jordan don duba wurare masu tsarki da gudanar da addu’o’i.
Shugaban hukumar ta kasa, Rev. Yakubu Pam ne ya bayyana hakan yayin da yake ban-kwana wa kashin farko na masu zuwa aikin ibadar daga jihohin Bauchi, Gombe da Filato, karon farko tun bayan bullar cutar coronavirus a duniya.
Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya ce gwamnati na daukar dawainiyar masu zuwa ayyukan ibadar ne don su je su gudanar da addu’oi ga kasa.
Saurari rahoto cikin sauti daga Zainab Babaji: