Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Tsaro Sun Ce Za Su Kama Masu Ta Da Husuma A Jihar Filato


Gwamna Simon Lalong
Gwamna Simon Lalong

Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta ce ta gano wasu shugabanni da aka ba su beli ake kuma mika yatsa a kansu kan hare-haren da aka yi a wasu sassan arewacin jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Filato, Edward Egbuka ne ya shaida wa manema labarai bayan wani taron gaggawa da gwamnatin jihar ta kira don dakile matsalolin tsaro da suka kazanta a kananan hukumomin Bassa da Riyom a jihar.

A cewar Egbuka, tuni sun ruga sun baza jami'ansu a yankunan da rikicin ya faru domin kaucewa yaduwarsa a sassan jihar.

Kwamishinan yada labarai da sadarwa a jihar Filato, Mr. Dan Manjang ya ce gwamnati na iya kokarinta wajen wanzar da zaman lafiya a jihar.

Ya kara da cewa ya rage wa wadanda ke da hurumin aiwatar da hukunci ne su aiwatar kan wadanda aka kama ake tuhuma da haddasa rikicin.

"Akwai wadanda ma har an kama, an kai su gaban kuliya, an ba da belinsu, kinsan yadda harkokin dokokin namu suke a Najeriya, ba ka da hurumin ka ajiye mutum na wasu kwanaki, sai ka ga kungiyoyi daban-daban suna harararka" In ji Manjang.

"Har yanzu mutanen da ake kama su da irin wadannan dabi'u ba a hukukta su ba, wannan alhaki ya hataya a wuyan 'yan sanda da kotuna." ya kara da cewa.

Rikicin na kwanan nan tsakanin Fulani da kabilar Irigwe ya yi sanadin rasa rayuka, kone gidaje, lalata amfanin gonaki da dabbobi.

Saurari rahoto cikin sauti daga Zainab Babaji:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00


XS
SM
MD
LG