Masu zanga zanga sun yi taro a Washington a jiya Asabar domin nuna goyon baya ga shugaba Donald Trump da zargin da ya yake yi na tabka magudi a zaben ranar 3 ga watan Nuwamba da babu hujja.
Jiya Lahadi, a karon farko, Shugaban Amurka Donald Trump ya nuna ya amince da cewa dan takarar Demokrat Joe Biden "ya lashe" zaben shugaban kasa kusan makonni biyu da suka gabata, amma sanadiyyar magudi.
Babban jami’in zabe a jihar Georgia da ke kudancin Amurka ya ba da umarnin a sake kidayar kuri’un zabe da hannu wanda aka yi tsakanin Shugaba Donald Trump da zababben Shugaban Joe Biden.
Jami’an zabe a jihar Georgia da ke Amurka sun fara aikin sake kidaya kuri’un da aka kada a sassan jihar 159 a zaben shugaban kasar da aka yi a makon da ya gabata - amma wannan karon da hannu.
Yayin da ake ci gaba da kidayar kuri'u a zaben shugaban kasa a Amurka, kafafen yada labarai sun yi hasashen wanda ya lashe zaben.
Kamala Harris za ta kafa tarihi idan har ta kasance kamar yadda ake tsammani, Mataimakiyar Shugaban Kasar Amurka, mace ta farko bakar fata da zata zamo Mataimakiyar Shugaban Kasa a Amurka, da zata shiga jerin maza duka kuma farar fata da suka rike mukamin a tarihin Amurka
Babban Atoni Janar din Amurka William Barr ya ba masu shigar da kara na gwamnatin tarayya umurnin su binciki “tarin zarge-zarge” da ake yi kan tafka magudi a zaben shugaban kasar da aka yi a makon da ya gabata, matakin da ya sa daya daga cikin jami’in ma’aikatar shari’ar ya ajiye aikinsa.
Kwamitin mika Mulki na Joe Biden bai jira sanarwar sakamakon zaben shugaban kasa ba ya kama aiki gadan gadan.
Ratar da dan takarar jam’iyyar Democrat Joe Biden ya ba shugaban Amurka Donald Trump a kidayar kurin’n da ake yi a jihar Pennsylvania ta kara fadada.
VOA ta yi hasashen tsohon mataimakin shugaban kasa a Amurka, Joe Biden wanda ya dade ana damawa da shi a siyasar Amurka, shi ne ake gani zai lashe zaben shugaban kasar, abin da ke nufin za a rantsar da shi a matsayin shugaban kasa ranar 20 ga watan Janairun 2021.
Jama’a na ci gaba da bayyana matsayinsu bayan da kafafen yada labaran Amurka suka yi hasashen dan takarar jam’iyyar Democrat Joe Biden ne ya lashe zaben Shugaban kasar Amurka duk da cewa dan takarar jam’iyyar Republican Shugaba Donald Trump bai amince da sakamakon ba.
Kasar koriya ta kudu ta taya Joe Biden na jam’iyyar Democrat murna bisa nasarar da ya samu kan Shugaba Donald Trump a zaben shugaban kasar Amurka mai zafi da aka yi.
Domin Kari
No media source currently available