Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Ce Kada Biden Ya Kuskura Ya Ce Shi Ya Lashe Zabe


Shugaba Donald Trump, hagu da Joe Biden, dama
Shugaba Donald Trump, hagu da Joe Biden, dama

Ratar da dan takarar jam’iyyar Democrat Joe Biden ya ba shugaban Amurka Donald Trump a kidayar kurin’n da ake yi a jihar Pennsylvania ta kara fadada.

Tazarar ta karu ne daga 5,000 da aka gani da safiyar ranar Juma’a zuwa kusan dubu 29 a daren ranar, kuma ana hasashen za ta ci gaba da karuwa yayin da ake ci gaba da kidayar.

Hakan kuma zai ba Biden damar kai wa adadin kuri’u 270 da ake bukata daga kwalejin masu zabe kafin dan takara ya samu nasara.

Hakazalika, Biden na gaba-gaba a kidayar da ake yi a jihar Georgia da kuri’a sama da 4,000 yayin kuma da yake da kwakkwarar tazara a jihohin Arizona da Nevada.

Ko da yake, har yanzu ba a yi hasashen wanda zai lashe wadannan jihohi ba a tsakanin ‘yan takarar biyu ba.

Yayin da yake magana da magoya bayansa a ranar Juma’a, Biden ya ki ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben.

Idan har ya yi nasarar lashe Pennsylvania, adadin kuri’unsa a kwalejin masu zabe zai kai 273 kenan, sama da na Trump, wanda ke da 214.

"Ba mu da wani shirin ayyana samun nasara tukuna, amma alkaluman da mu ke gani, suna kara mana kwarin gwiwar cewa, mu za mu lashe wannan zabe." In ji Biden.

Shi kuwa shugaba Trump ya ba Biden rata a sauran jihohin North Carolina da Alaska da su ma ba a kammala ba.

Amma idan har bai lashe Pennsylvania ba, ko da ya yi nasara a sauran jihohin, Trump ba zai shiga gaban Biden a yawan kuri’un ba.

A ranar Juma’a Trump ya shiga shafinsa na Twitter ya gargadi Biden, da kada ya yi sammakon ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben, yana mai cewa yanzu ne ma ya fara shigar da kararraki a gaban kotun inda za su kalubalanci zaben.

A dai ranar zabe Trump ya yi ikrarin cewa shi ya lashe zaben.

“Kada Joe Biden ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa bisa kuskure, ni ma zan iya wannan ikrarin, domin yanzu ne ma muka fara shigar da kararraki.” Trump ya ce a sakon da ya wallafa a Twitter a ranar Juma’a.

Gangamin yakin neman zaben Trump na kalubalantar kuri’un da ake kadiyawa ne a wasu jihohi da dama, kamar yadda ya fada a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.

"Ba a kammala wannan zabe ba." Sanarwar ta nuna.

Ta kuma kara da cewa, a karshe za a ayyana shugaba Trump a matsayin wanda ya lashe zaben idan aka sake kirga kuri’un wasu jihohi da aka yi kusan kunnen doki.

Sannan kararrakin da suka shigar kan zargin an tafka magudi duk da cewa ba a tantance zargin ba, ita ma wata dama ce da za ta ba su nasara.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG