Jama'a a fadin Amurka su na kada kuri'a a ranar karshe ta zaben shugaban kasar na 2020. Tuni miliyoyin 'yan kasar suka kada kuri'unsu da wuri kafin ranar zaben, Talata.
Dokar kasar Amurka ta ba ‘yan ci rani da ke da izinin zama ‘yan kasa ‘yancin zabe da kuma tsayawa takara kamar sauran Amurkawa. Damar da mutane da dama su ke dauka da muhimmanci
A yayin da kasashen duniya suka maida hankali kan kasar Amurka don ganin yadda zaben kasar ke gudana a gefe guda kuma masharhanta na ci gaba da yin sharhi, sun ce zaben ma’auni ne kan yadda tattalin arzikin duniya da kuma zaman lafiya zasu kasance.
Da sanyin safiyar yau Talata masu kada kuri’a zasu fita zuwa runfunan zabe don zabar gwaninsu inda zasu jure layi mai tsawo don ganin sun yi amfani da ‘yancin da dokar kasa ta basu na zabar wanda zai shugabance su.
A yau 3 ga watan Nuwamba, masu kada kuri’a a New Jersey, zasu yanke hukunci kan ko a halatta amfani da tabar Wiwi a hukumance.
A ranar jajiberin zaben Shugaban kasa a Amurka masana harkokin siyasa a Nigeria sun ci gaba da yin sharhi kan babban zaben da za a yi ranar Talata 3 ga watan Nuwamba.
A Amurka mutane sama da miliyan 90 sun riga sun kada kuri’unsu ta hanyar wasika, mun leka wani wajen zabe inda wasu Alkalan Kotu biyu, Chief Judge Sairah Butt da Chief Judge Robin Burgett, suka yi mana bayanin cewa ko mai na tafiya yadda ya kamata, da matakan da aka dauka don kare lafiyar jama’a.
Yayin da hankalin kasashen duniya ya karkata kan zaben shugaban kasa na Amurka da za a yi ranar Talata 3 ga watan Nuwamba masu rajin kare dimokradiyya da masu bin diddigin siyasar duniya a Nijer na ci gaba da bayyana matsayinsu game da yadda suke kallon zaben.
Domin Kari
No media source currently available