Yayin da ake ci gaba da dakon sakamakon zaben shugaban Amurka, jama'a a nahiyar Afirka na ci gaba da bayyana ra'ayoyi mabanbanta kan yadda suke kallon wannan zabe mai cike da tarihi.
Ana ci gaba da kirga kuri'u a jihohin da ke gabar Amurka ta Gabas da duk fadin kasar, bayan da Amurkawa suka yanke shawarar ko za su bai wa shugaban kasa Donald Trump na jam’iyyar Republican wani wa'adin shekaru hudu, ko kuma su mika Fadar White House ga dan takarar jam’iyyar Democrat Joe Biden.
Ana ci gaba da dakon sakamakon zabe na Muhimman Jihohi da 'yan takara a Zaben na Amurka Donald Trump dan Republican, mai neman wa'adi na biyu da Joe Bide na Jam'iyar Democrat, ke zawarcinsu don cin kujerar shugabancin kasa.
Masu zanga zanga sun fito a garuruwa da dama jiya Laraba don kiran da a kammala kirga kuri’un zaben shugaban Amurka.
Da dama daga cikin mafusatan ‘yan Republican magoya bayan Shugaba Donald Trump sun hallara a cibiyoyin kidaya kuri’un a Detroit da Phoenix yayin da aka bada sakamakon zaben a ranar Laraba a manyan jihohin biyu, yayin da dubban masu zanga-zangar magoya bayan shugaban ke neman a dakatar da kidaya
Ga 'yan kasashen Afirka da yawa da ke zaune a Amurka, ‘yancin kada kuri’a wani abu ne mai daraja.
Mata a Amurka suna taka muhimmiyar rawa a zaben shugaban kasa, sukan kuma gudanar da gangami a duk fadin kasar gabanin zabe da nufin fadakar da ‘yan’uwansu kan muhimmancin zaben
Domin Kari
No media source currently available
Bilkisu Nana Hassan, wata ma’aikaciyar gwamnati da ta yi ritaya a Kaduna, ta ce mata za su iya rungumar yin noma na zamani a cikin gidajensu, ba tare da sun je ko ina ba.