A ranar Litinin Barr ya aike da wasiku ga masu gabatar da kararrakin wadanda wasu kafafen yada labaran Amurka da dama suka samu kwafi, amma kuma ba sa dauke da wani takamaiman misali da ya nuna cewa an tafka magudi a zaben.
A cewar Barr, za a iya kaddamar da bincike “idan akwai misalai karara da suka nuna cewa an tafka magudi, wadanda idan da gaske ne, za su iya shafar sakamakon zabe na tarayya da aka yi a mataki na jiha.
Babban Atoni Janar din ya kara da cewa, “duk da cewa yana da muhimmacni a saurari zarge-zarge da ke da tushe a lokacin da ya dace ta hanya madaidaiciya, yana kuma da kyau jami’an ma’aikatar su yi taka-tsan-tsan, su ga cewa sun yi adalci tare da gujewa nuna goyon baya ga wani bangare ko jam’iyya.”
Shi dai Shugaba Donald Trump bai amsa cewa an ka da shi a zaben ba, ya kuma yi ikrarin cewa an tafka magudi wajen kada kuri’a a jihohi da dama, sai dai bai gabatar da wata hujja da ta nuna gaskiyar hakan ba.
Manyan kafofin yada labarai sun ayyana Biden a matayin wanda suka yi hangen shi zai lashe zaben, bisa alkaluman da jihohi suka fitar.
Facebook Forum