Ratar da dan takarar jam’iyyar Democrat Joe Biden ya ba shugaban Amurka Donald Trump a kidayar kurin’n da ake yi a jihar Pennsylvania ta kara fadada.
VOA ta yi hasashen tsohon mataimakin shugaban kasa a Amurka, Joe Biden wanda ya dade ana damawa da shi a siyasar Amurka, shi ne ake gani zai lashe zaben shugaban kasar, abin da ke nufin za a rantsar da shi a matsayin shugaban kasa ranar 20 ga watan Janairun 2021.
Jama’a na ci gaba da bayyana matsayinsu bayan da kafafen yada labaran Amurka suka yi hasashen dan takarar jam’iyyar Democrat Joe Biden ne ya lashe zaben Shugaban kasar Amurka duk da cewa dan takarar jam’iyyar Republican Shugaba Donald Trump bai amince da sakamakon ba.
Kasar koriya ta kudu ta taya Joe Biden na jam’iyyar Democrat murna bisa nasarar da ya samu kan Shugaba Donald Trump a zaben shugaban kasar Amurka mai zafi da aka yi.
Bayan da kafofin yada labaran Amurka suka yi hasashen cewa dan takarar jam'iyyar Democrat Joe Biden ne ya lashe zaben Shugaban kasar 'yan Najeriya suka fara bayyana ra'ayoyinsu.
Dan takarar jam’iyyar Democrat Joe Biden ya kara kusantar yiwuwar samun nasarar lashe zaben shugaban Amurka yayin da alkaluman da aka sabunta suka nuna ya tserewa Shugaba Donald Trump a jihohin Georgia da Pennsylvania.
Mutane sun mayar da martani bayan kafofin yada labarai sun sanar cewa dan takarar shugabancin Amurka na Democrat Joe Biden ya lashe zaben shugaban kasar Amurka na 2020
Yayin da ake ci gaba da dakon sakamakon zaben shugaban Amurka, jama'a a nahiyar Afirka na ci gaba da bayyana ra'ayoyi mabanbanta kan yadda suke kallon wannan zabe mai cike da tarihi.
Ana ci gaba da kirga kuri'u a jihohin da ke gabar Amurka ta Gabas da duk fadin kasar, bayan da Amurkawa suka yanke shawarar ko za su bai wa shugaban kasa Donald Trump na jam’iyyar Republican wani wa'adin shekaru hudu, ko kuma su mika Fadar White House ga dan takarar jam’iyyar Democrat Joe Biden.
Ana ci gaba da dakon sakamakon zabe na Muhimman Jihohi da 'yan takara a Zaben na Amurka Donald Trump dan Republican, mai neman wa'adi na biyu da Joe Bide na Jam'iyar Democrat, ke zawarcinsu don cin kujerar shugabancin kasa.
Domin Kari
No media source currently available
Bilkisu Nana Hassan, wata ma’aikaciyar gwamnati da ta yi ritaya a Kaduna, ta ce mata za su iya rungumar yin noma na zamani a cikin gidajensu, ba tare da sun je ko ina ba.