Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gudanar Da Tarukan Goyon Bayan Trump Da Zarginsa Na Magudin Zabe


Magoya bayan Trump a Washington.
Magoya bayan Trump a Washington.

Masu zanga zanga sun yi taro a Washington a jiya Asabar domin nuna goyon baya ga shugaba Donald Trump da zargin da ya yake yi na tabka magudi a zaben ranar 3 ga watan Nuwamba da babu hujja.

An gudanar da taruka da dama a ranar, ciki har da tattakin mutum miliyan daya na mata masu goyon bayan Trump da kuma wata zanga zanga mai lakabi “Stop the Steal” da suke zargi mara tushi na tabka magudi a zaben shugaban kasa.

Trump da yaki amincewa da shan kaye a zaben shugaban kasa da zababben shugaba Joe Biden ya masa, ya ce akwai rashin gaskiya da dama da aka tabka a jihohin da basu zabe wuri daya. Jami’an zaben jihohin sun ce babu wani magudi da aka tabka da zai iya sauya sakamakon zaben.

Ana gudanar da zanga zangar ne a lokacin da ake hasashen cewa Biden ya samu gagarumar nasara tare da samun kuru’un wakilai sama da 270 da masu takara ke nema su lashe zabe.

Ana saura kimanin sa’o’I biyu a fara tarukan gangamin, Trump ya zaga da motoci a kan hanyar Pennsylvania Avenue a Washington, yana murmushi yana cira hannu ga masu zanga zangar da suka zo su nunawa shugaban kasa goyon baya.

Matukan Babura dake gaban shugaban kasar sun jagorance shi zuwa filin wasan kwallon golf na takwararsa dake kusa da arewacin jihar Virginia. A kan hanyarsa ta komawa fadar White House, shugaban kasar ya sake bi inda mutanen suke ya yi musu shewa na nuna goyon baya, a cewar labaran Fox.

Masu gabatar da shirye shirye a kafafen labarai na masu ra’ayin mazan jiya da kuma masu kishin kasa ne suka shirya tarukan gangamin, hakan kuma yasa kungiyoyin rajin yaki da wariyar launin sun shirya maida martani da wasu zanga zangar kin jinin wariyar launi da akidar fifita farar fata. Rahotanni sun ce an dan samu kana rashin fahimta.

Trump ya fitar da wani sakon Twitter a ranar Juma’a, na nuna jinjina ga goyon baya da yake samu, musamman tarukan da ake gudanarwa a fadin kasar, ciki har da gagarumin taron na jiya Asabar da aka gudanar a Washington D.C. Har ma yace tana yiwuwa ya je ya gaisa dasu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG