Yadda yanayin al’umar Amurka ke sauyawa ya karawa tsirarun al’umomi da ba fafaren fata ba kwarin gwiwar neman takarar mukamai – ciki har da sabbin zuwa.
Shugaban Amurka Donald Trump ya fadawa manema labarai a jiya Laraba cewa kuru’un da yake samu a jihohin da ake kira da filin daga sun haura manyan binciken jin ra’ayi dake nuna tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden na kasa shi.
Ku kalli muhawara ta karshe ta ‘yan takarar shugaban kasa a Amurka tsakanin Joe Biden da Shugaba Donald Trump.
Yan takarar Shugaban kasar Amurka sun bayyana abinda ya banbanta su da kuma yadda za su tinkari muhimman matsalolin da suka tsonewa Amurkawa Ido
Yau alhamis za a gudanar da muhawara ta biyu kuma a karshe tsakanin 'yan takarar shugaban kasar Amurka kafin zaben shugaban kasa da za a gudanar ranar uku ga watan Muwamba.
Ku kalli muhawarar mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa a Amurka tsakanin Sanata Kamala Harris ta jam’iyyar Democrat da Mike Pence na jam’iyyar Republican.
Jiya Lahadi shugaban Amurka Donald Trump da mai kalubalantarsa na jam’iyyar Democrat Joe Biden suka yi zawarcin masu jefa kuri’ar farko a jihohin da ake fafatawa jihar Nevada da North Carolina, yayin da muhawarar karshe ta shugaban kasa ke karatowa a wannan makon.
Mata sun gudanar da gagarumin gangami jiya asabar a birane daban daban na fadin kasar da nufin karfafawa Amurka guiwa su fita zaben shugaban kasa da za a gudanar ranar uku ga watan Nuwamba.
Shugaban Amurka Donald Trump na jam’iyyar Republican da abokin adawarsa na jam’iyyar Democrat Joe Bidden sun koma yakin neman zabe ranar Juma’a 16 ga watan Oktoba bayan da kowannensu ya yi taron amsa tambayoyin masu kada kuri’a a wurare daban-daban wanda aka nuna ta talabijin.
Duk da yake shugaban Amurka Donald Trump na fuskantar koma baya a kuru’un jin ra’ayoyin jama'a, to amma ya na ci gaba da samun goyon baya a yankunan karkara. inda manoma suke kuma suka samu taimakon da gwamnati ta yiwa sashen noma.
Muhawara da aka tafka tsakanin mataimakan 'Yan takarar Shugaban kasar Amurka da ta kasance daya tilo da zasu yi kafin zaben shugaban kasa, ta tabo batutuwa da dama da suke sosawa Amurka rai.
Domin Kari
No media source currently available