Marigayi tsohon shugaban Amurka Jimmy Carter, manomin gaydar da ya lashe zaben shugaban kasar Amurka bayan rikicin Watergate da yakin Vietnam ya mutu a watan Disamban 2024 yana da shekaru 100 a duniya.
Shugaba Trump ya yi nuni da cewa za'a sanya wasu karin haraji a makonnin masu zuwa.
Fitacciyar mawakiyar dai ba ta taba lashe kyautar kundin wakoki ba duk da lashe kyautar Grammy 32, fiye da kowane mawaki.
Akalla mutane bakwai ne suka mutu a lokacin da wani jirgin saman daukar marasa lafiya ya fado a Philadelphia ranar Juma'a, ciki har da 'yan Mexico shida da ke cikin jirgin da kuma mutum daya da ke kasa, in ji shugabar Mexico da kuma magajin garin Philadelphia ranar Asabar.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai dora kashi 10 cikin 100 kan danyen man Canada daga yau Asabar. Sauran kayayyakin Canada za su sha harajin kashi 25 cikin 100.
Yiwuwar janye tallafin Amurka a duniya na janyo muhawara a ciki da wajen kasar
Yayin da duniya ke ci gaba da fama da rikice rikice, wasu masu ruwa da tsaki na fatan manufofin Amurka karkashin Trump, na rage daukar matakan soji, zai taimaka wajen kawo kwanciyar hankali
Jami’an Amurka sun bayyana cewar zai yi wuya a samu sauran mai rai bayan da wani karamin jirgin saman fasinja dauke da mutane 64 yayi karo da wani shelkwaftan soja a sarari samaniya tare da rikitowa cikin ruwan kogin Potomac na birnin Washington da ya fara kankarewa.
Ma’aikatan ba da agaji 300 ke cikin aikin ceton-da aka gudanar da galibinsa cikin tsananin duhu da sanyi.
Bayan jirgin saman farar hula mai dauke da fasinjoji 64 da kuma jirgin sama mai saukar ungulu na soji sun yi karo a sararin sama sun fado, ana fargabar cewa rayuka sun salwanta.
An shiga cece kuce bayan da Shugaba Donald Trump ya yi amfani da ikonsa na shugaban kasa wajen kawo karshen zama dan kasa ta wajen haihuwa.
Domin Kari