Magajin garin Philadelphia Cherelle Parker, ya shaidawa taron manema labarai cewa mutumin da ya mutu a kasa yana cikin wata mota a wurin da hadarin ya afku.
“Ya zuwa yanzu, kididdigar mu ita ce, akwai mutane 19 da suka jikkata,” in ji Parker.
A waje daya kuma, shugabar kasar Mexico Claudia Sheinbaum, ta fada a cikin wani sako ta shafin X cewa ta bukaci jami'an ofishin jakadancin da su tallafa wa iyalan 'yan kasar Mexico shida da ke cikin jirgin kuma suka mutu a lokacin da ya fado.
Jirgin daukar marasa lafiyar, wanda ke da hedikwata a Mexico kuma yana da lasisin yin aiki a Amurka, a ranar Juma'a ya ce jirginsa ya yi hatsari tare da ma'aikatan jirgin guda hudu, majinyacin likitan yara daya da mahaifiyar mara lafiyar a cikin jirgin.
Tun farko dai an bada rahotan duk wadanda ke cikin jirgin sun fito ne daga Mexico. Wadanda suka mutu sun hada da wata yarinya da ke karbar magani a wani asibitin Philadelphia da mahaifiyarsa.
Akalla mutane shida a kasa suka jikkata a hatsarin na ranar Juma'a.
Shugaba Sheinbaum ta bayyana ta'aziyya da safiyar yau Asabar a cikin wata sanarwa ta dandalin sada zumunta na X.
“Na yi jimamin mutuwar wasu ‘yan Mexico shida a hadarin jirgin sama a birnin Philadelphia na Amurka. Hukumomin ofishin jakadancin suna ci gaba da tuntubar iyalai; Na nemi Sakataren Harkokin Waje ya tallafa duk abin da ake bukata.” in ji ta a cikin wata sanarwa da aka rubuta cikin harshen spaniya.
Jirgin na jigilar marasa lafiya ya dauko wata yarinya da ta kammala jinya a asibitin yara na Shriners, da mahaifiyarta da wasu mutane hudu. Jirgin ya fado ne a wata unguwa ta birnin Philadelphia jim kadan bayan tashinsa da yammacin Juma'a, inda ya haddasa wata gobara da ta lakume gidaje da dama.
Dandalin Mu Tattauna