Trump ya ce zai dora harajin kashi 25 cikin 100 a kan kayan da ake shigowa dasu daga Canada da Mexico da kuma harajin kashi 10 cikin 100 a kan kaya daga kasar China
“Kasashen Canada da Mexico suna bada damar kwararan bakin haure da haramtacciyar kwayar nan ta Fentanyl a cikin kasarmu kuma tana kashe Amurkawa,” in ji sakatariyar jarida ta fadar White House Karoline Leavitt, tana fada yayin wani taron 'yan jarida a jiya Juma’a.
Leavitt bata ce ko akwai wata kasa da za a kebeta a wannan matakin ba. Ta ce “wannan alkaura ne da aka dauka wanda kuma shugaban kasa ya rike su.”
Yayin da ‘yan jarida suka tambaye shi jiya Juma’a, Trump ya ce kasashen uku ba za su iya sauya shawarar da ya dauka ba kuma babu wani abin da za a yi a kan batun harajin da zai kakaba musu.
Trump ya ce zai dora kashi 10 cikin 100 kan danyen man Canada daga yau Asabar. Sauran kayayyakin Canada za su sha harajin kashi 25 cikin 100.
Shugaban kasar ya lashi takobin dora haraji a kan injin komputa, kayayyakin magani, karafe da farin karfe da kuma mai da iskar gas.
Za a dora haraji kan mai da iskar gas a ranar 18 ga watan Faburairu, in ji shugaba Trump. Ya kuma bayyana alamun saka haraji kan sauran kayayyakin a cikin ‘yan makwanni masu zuwa, ba tare da bada ranaku ba.
Dandalin Mu Tattauna