Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Beyonce Tana Sake Takarar Lashe Babbar Kyautar Grammy Da Za'a Yi Yau Lahadi


KYAUTUTTUKAN GRAMMY
KYAUTUTTUKAN GRAMMY

Fitacciyar mawakiyar dai ba ta taba lashe kyautar kundin wakoki ba duk da lashe kyautar Grammy 32, fiye da kowane mawaki.

Yau Lahadi za’a gudanar da bikin bayar da kyaututtuka na Grammy Awards a birnin Los Angeles da ke jihar California a nan Amurka, a wani bikin da za'a karrama mafi kyawun kidan da ya yi fice, tare da amincewa da mummunar gobarar daji da ta yi barna a masana’antar

Beyonce za ta yi gasa don samun babbar kyautar Grammy da kundin wakokin ta na shekara tare da “Cowboy Carter.”

Fitacciyar mawakiyar dai ba ta taba lashe kyautar kundin wakoki duk da lashe kyautar Grammy 32, fiye da kowane mawaki.

Har ila yau, a cikin wadanda suke takarar kundin wakokin na shekara akwai shahararriyar mawaki ya Taylor Swift da “The Torture Poets Department” da Billie Eilish da “Hit Me Hard and Soft.”

Tashar talabijin ta CBS za ta watsa bikin kai tsaye da misalin karfe 8 na dare agogon ET wato karfe 1 agogon GMT na ranar Litinin daga Crypto.com Arena da ke Los Angeles.

Dan wasan barkwanci Trevor Noah ya dawo don gabatar da shirin na talabijin, wanda zai kasance wani bangare na shirin bayar da kyaututtuka, tara kudade ga mawaka da kuma sauran wadanda gobarar ta shafa.

Daruruwan mutane da ke sana’ar waka na daga cikin wadanda suka rasa gidajensu a bala’in.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG