Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Sanya Hannu Kan Umarnin Zartarwa Na Kakaba Haraji Kan Canada, Mexico Da China


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaba Trump ya yi nuni da cewa za'a sanya wasu karin haraji a makonnin masu zuwa.

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu kan umarnin zartarwa da ke daura harajin kashi 25 cikin 100 kan kayayyakin da ake shigo wa da su daga kasashen Canada da Mexico da kuma harajin kashi 10 cikin 100 na kayayyakin da ake shigowa da su daga China, wanda zai fara aiki a ranar Talata mai zuwa, a cewar fadar White House.

Sakatariyar yada labaran fadar White House, Karoline Leavitt, ta fada a yayin wani taron manema labarai a ranar Juma’a cewa, “Canada da Mexico suna ba da damar shigar da muguwar kwayar nan ta fentanyl da ke kashe Amurkawa da kuma bakin haure ba bisa ka’ida ba zuwa kasar mu.”

Trump, wanda yake hutun karshen mako a wurin shakatarwa sa na Mar-a-lago da ke jihar Florida, bai shirya zai yiwa manema labarai magana ba.

Yayin da kayayyakin Canada za su sha haraji kashi 25 cikin 100, Trump ya ce zai daura haraji kashi 10 cikin 100 kan danyan man Canada da ake shigo da shi. Makamashin da ake shigo wa da shi daga Mexico na cikin kayayyakin da aka daurawa harajin kashi 25 cikin 100.

A karkashin wannan umarni, babu wani neman sassauci, amma akwai abu daya na kara yawan kudaden haraji idan kasashen suka mayar da martani.

Mexico da Canada sun mayar da martani daga baya a ranar Asabar, yayin da China ta yi tir da matakin na Trump a ranar Lahadin nan, amma ta bar damar tattaunawa don gujewa tabarbarewar lamarin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG