Shugaban Amurka Donald Trump ya yi shelar labta wasu nau’ukan haraji, da tsauraran matakan VISA, da kuma sauran wasu matakai na ramuwar gayya kan kasar Colombia, bayan da ta ki yadda wasu jiragen sojin Amurka biyu, dauke da bakin haure, su sauka a kasar.