Kamfanin Apple ya amince ya biya kudi dalar Amurka miliyan 95, domin sasanta karar da ake zargin kamfanin mai na’urorin lekon sirri, da yin amfani da na’urar saukaka amfani da waya ta Siri don satar jin maganar mutane masu amfani da wayoyin iPhone da sauran na'urorin zamani na kamfanin.
Matsayar da aka gabatar a ranar Talata, za ta sasanta karar da ta shafi zargin cewa, kamfanin na Apple ya saita na’urar ta Siri da gangan domin ta rika nadar tattaunawar mutane ta hanyar wayoyin salula na iPhone, da sauran na'urorin da aka sanya musu ita tsawon fiye da shekaru goma.
Idan an amince da sulhun, dubun-dubatar masu amfani da wayoyin salula na iPhone da sauran na'urorin Apple daga ranar 17 watan Satumban shekarar 2014, zuwa ƙarshen shekarar da ta gabata, za su iya gabatar da ƙara.
Kowanensu kuma, zai iya samun karɓar kudi har zuwa $20 akan kowace na'ura mai manhajar Siri.
Dandalin Mu Tattauna