Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akalla Mutane 24 Ne Suka Mutu Yayin Da Ake Ci Gaba Da Yakar Gobara A Los Angeles


California Wild Fires
California Wild Fires

Gobara ta mayar da unguwanni tamkar guma-gumai masu ci da wuta, inda ta hadiye gidajen attajirai da fitattun mutane da talakawa baki daya, tare da mayar da wurin kamar an yi yaki. Jami'ai sun ce akalla gine-gine 12,300 sun lalace ko konewa kurmus.

Akalla mutane 24 ne suku mutu a al'amarin da gwamnan California Gavin Newsom ya bayyana da mafi munin bala'i a tarihin Amurka, wanda ya lalata dubban gidaje tare da tilastawa mutane 100,000 arcewa.

Jami'an kashe gobara na kokarin shawo kan wutar dajin dake ci a bangarori 2 tsawon kwanaki 6 a jere a jiya lahadi, inda suke cin gajiyar 'yar lafawar da aka samu daga yanayi mai hatsari gabanin kadawar iskar da ake sa ran ta sake ruruta wutar.

Gobara ta mayar da unguwanni tamkar guma-gumai masu ci da wuta, inda ta hadiye gidajen attajirai da fitattun mutane da talakawa baki daya, tare da mayar da wurin kamar an yi yaki. Jami'ai sun ce akalla gine-gine 12,300 sun lalace ko konewa kurmus.

Palisades ita ce unguwa ta biyu mafi arziki a Los Angeles, California inda wasu jaruman masana'antar shirya fina finai ta Hollywood suka tsere daga gidajensu inda wasu kamar John Goodman, Anthony Hopkins, Miles Teller, Anna Ferris, Paris Hilton, suna kallon yadda gidajensu suka kone kurmus

Lardin Los Angeles ya sake shiga wani dare na tashin hankali da karayar zuciya," a cewar jami'i mai kula lardin Los Angeles Lindsey Horvath.

Masu kashe gobara ta jiragen sama, wasu daga ciki na kwarfar ruwa daga tekun pacific, tare da zubo shi da magungunan kashe yayin da jami'an dake kasa ke amfani da mesar ruwa da sauran kayan kashe gobara domin kare wutar dake ci a yankin Palisades daga fadada zuwa yankin tsaunukan Brentford da sauran sassan Los Angeles dake da dandazon jama'a.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG