Yayin da nazarin yin zabe ta hanyar aika sakonni ta gidan waya a Amurka ke janyo ce-ce ku-ce, shugaban hukumar aika sakonnin ya bayyana a gaban majalisar dattawan kasar.
Bayan shafe kusan rabin karni a fagen siyasar Amurka, a jiya Alhamis da daddare, Joe Biden ya amince da ya zama dan takarar shugaban kasar Amurka a zaben 3 ga watan Nuwamba,
Ma’aikatar shari'ar Amurka ta tuhumi wasu mutane 3, wadanda ake zargi da hannu a wata badakala da masu shigar da kara suka ce yunkuri ne na fitarwa da shugaban addinin Iran daloli daga Amurka.
Yau Litinin Yan Jam’iyar Democrat a nan Amurka zasu kadamar da babban taron jamiyar na kwanaki hudu da za’a gudanar ta yanar gizo.
Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a jiya Asabar cewa zai jarraba daukar wani mataki mai tsarkakiya na maido da takunkuman Majalisar Dinkin Duniya a kan Iran, bayan kwamitin sulhun majalisar ya yi watsi da bukatar Washington na kara lokacin haramcin hada hadar makamai a kan Jamhuriyar Islamiya.
Amurka da Korea ta Kudu za su fara atisayen soji na hadin gwiwa na shekara-shekara da suka saba yi a ranar Talata mai zuwa.
Amurka da kasar Poland sun sanya hannu a kwanan nan a kan tattaunawar inganta yin aiki tare a kan tsaro a jiya Asabar a birnin Warsaw.
Adadin gwajin tabbatar da cutar coronavirus a Amurka a duk rana ta Allah yayi kasa a karon farko, duk da kira sashen kiwon lafiyar jama’a da jami’an tarayya ke yi da a kara yawan gwaje gwaje a Amurka.
Yawaitar annobar COVID-19, yasa birane da garuruwa a fadin Amurka suna fama da rashin isasshen haraji, lamarin dake barazana ga katsewar ayyukan bukatun mazauna garuruwan da suka dade suna dogaro a kai.
Yayin gabatar da abokiyar takarar sa dan takarar shugaban kasa na jam'iyar Democrats ya caccaki shugaba Donald Trump da mataimakinsa Mike Pence akan kasa shugabanci na gari a lokacin annobar COVID-19, inda ya ce shi da Harris za su gyara barnar da aka yi.
Jihohi biyar na Amurka suna gudanar da zabuka a jiya Talata, da ya hada da 'yar majalisa daga jihar Minnesota Ilhan Omar, babbar mai sukar Shugaba Donald Trump, ta fuskantar kalubale mai tsauri a zaben fidda gwani na jam’iyyar Democrat a gundumar Minneapolis.
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo da takwaran aikinsa Anze Logar na Slovenia, sun rattaba hannu kan wata matsaya da aka cimma wacce ta shafi sabuwar fasahar samar da hanyar sadarwar intanet ta 5G.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.