Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DeJoy Ya Bayyana a Gaban Majalisar Dokokin Amurka


Babban shugaban Hukumar gidan waya ta Amurka, Louis DeJoy
Babban shugaban Hukumar gidan waya ta Amurka, Louis DeJoy

Yayin da nazarin yin zabe ta hanyar aika sakonni ta gidan waya a Amurka ke janyo ce-ce ku-ce, shugaban hukumar aika sakonnin ya bayyana a gaban majalisar dattawan kasar.

A yau Juma’a ne babban shugaban hukumar gidan wayar, Louis DeJoy, ya fada wa ‘yan majalisar cewa ba su sauya yadda suke tafiyar da aikin zabe ta hanyar tura sako ba kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

Ya kuma ce "yana mai tabbatar wa jama’a cewa za su kula da kuri’u kuma za su isa kan kari a zaben da za a yi a watan Nuwamba."

Amma a lokacin da ya bayyana karon farko a gaban majalisar tarayyar kasar, DeJoy ya ce yana duba yiwuwar yin sauye-sauye sosai don taimakawa hukumar wajen samun kudaden tafiyar da ita amma bayan an kammala zaben ranar 3 ga watan Nuwamba.

A ranar Talata Dejoy ya dakatar da matakan tsuke bakin aljihun da ya dauka, bayan da suka haifar da jinkiri wajen gudanar da ayyuka hukumar.

Louis DeJoy (hagu) tare da wani dan sanda (dama) bayan ya gama tattaunawa da kakakin majalisar wakilai, Nancy Pelosi
Louis DeJoy (hagu) tare da wani dan sanda (dama) bayan ya gama tattaunawa da kakakin majalisar wakilai, Nancy Pelosi

Jinkirin da aka samu ya kawo damuwa kan cewa miliyoyin kuri’un da za a tura ta sako zuwa hukumar, ta yi wu ba za a samu damar kirga su ba a zaben na watan Nuwamba, tun da kusan rabin masu kada kuri’a na Amurka za su aika da kuri’unsu ta akwatin gidan waya ne.

DeJoy, wanda ya ba da gudunmowar miliyoyin kudade ga Trump da sauran ‘yan Republican, ya ce bai yi magana da kwamitin yakin neman zaben Trump ko jami'a a Fadar White House Mark Meadow ba kan ayyukan ofishin na tura sakonni ba.

DeJoy ya ce jami’an hukumar za su aika kuri’u kashi 95 cikin 100 da aka tura ta hannunsu cikin kwanaki 3, kamar yadda aka yi a zaben ‘yan majalisar tarayyar kasar na shekarar 2018 a cewa Reuters.

Yayin zaman, ‘yan Republican da ke cikin kwamitin da suka hada da Sanata Ron Johnson na jihar Winsconsin da ke shugabantar kwamitin, sun kare matakan da DeJoy ya dauka, suna masu cewa lokaci ya yi da ya kamata a yi garanbawul kan kudaden da ake kashewa hukumar. Sun kuma zargi ‘yan Democrat da saka siyasa cikin lamarin.

A nasu bangaren, ‘yan Democrat da ke cikin kwamitin ciki har da Sanata Gary Peters na jihar Michigan, sun ce, damuwar da mutane ke nunawa kan jinkirin da ake samu wajen aikewa da sakonni a mazabar da yake wakilta, “ba labarin kanzon kurege ba ne.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG