Hukumar kula da yanayi ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce guguwar da aka yi wa lakabi da Laura, kawo yanzu ita ce guguwa mafi tsanani da muni a wannan shekara.
Jami’an kasar Cuba sun ce ana shirin sanya sabon matakin hana zirga zirgar jama’a da ababen hawa a matsayin wani bangare na kokarin rage yaduwar cutar coronavirus a Havana babban birnin kasar.
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi jawabinsa bayan amincewa da sake tsayawa takara a hukumance domin neman wa'adin mulki na biyu karkashin tutar jam'iyar Republican
Masana yanayi a nan Amurka sun yi hasashen isowar guguwa mai karfi da suka bayana a matayin mafi tsanani da ta taba ratsa Jihar Loiusiana .
Ana tuhumar matashi dan shekara 17 da lafin harbi da kisan ganganci, sabili da harbi da kuma kashe mutane biyu ya yin zanga zangar da ake gudanarwa dare uku a jere a Kenosha na jihar Wisconsin, biyo bayan harbe bakar fata da ‘yan sanda suka yi ranar Lahadi.
Kalaman uwargidar shugaban Amurka na daren jiya Talata yayin babban taron jam'iyyar Republican sun sha bamban da na mijinta, Shugaba Donald Trump, lamarin da ke ta ba masu nazari mamaki.
An harbe wani mutum har lahira yayin da aka shiga dare na uku a jere na zanga-zanga a garin Kenosha da ke jihar Wisconsin, saboda harbe wani Baƙar fata da 'yan sanda suka yi ranar Lahadi.
Wakilan babban taron jam’iyyar Republican na ta sauka a jihar North Carolina a wannan makon, inda saboda annobar coronavirus aka takaita adadin wadanda zasu halarci taron a zahiri da kuma wadanda za a gudanar ta yanar gizo.
Yayin da sama da jami’an kashe gobara dubu 12 ke ta kokarin shawo kan wata wutar daji da ke ci a California da ke Amurka, gwamnan jihar Gavin Newsom ya ce, ya nemi taimakon kasashen Canada da Australia, baya ga tallafin da ya nema daga gwamnatin tarayya.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.