Masu gabatar da jawabai zasu kasance a warwatse a fadin kasar, wadanda zasu yi kokarin taimakawa tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden samun nasarar a kan shugaba Donald Trump a zaben na watan Nuwamba.
Fitattun ‘yan democrats, ciki har da tsofaffin shugabannin Amurka Barack Obama da Bill Clinton da ‘yar takarar jam’iyar a 2016 Hillary Clinton , zasu yi jawabai akan cancantar Dan takarar mai shekara 77yrs Biden da mataimakiyarshi, sanato mai wakiltar Calofonia Kamala Harris, mace ta farko bakar fata kuma ta farko ‘yar kudancin Asiya Ba’amurkiya da babbar jam’iya ta tsayar takara a wannan matakin.
Wannan zai kasance babban taron siyasa na farko da Amurkawa suka taba gani da zai gudana ta yanar gizo ba tare da taron magoya bayan a jam’iyaun democrat da republicans suna wasa gwanayensu ko suka ba.
Biden zai yi jawabin amincewa da tsayawa takarar shugaban kasa karkashin tutar democrat a jiharsa ta Daleware ba tare da taro ba, sai ma’aikatansa da masu bashi shawara akan siyasa.
Facebook Forum